Sifeto Janar din rundunar ‘yan sandan Kasa Ibrahim Idris ya ce sun tsaro wasu hanyoyi da zasu ga cewa an shawo kan rikicin IPOB ba tare da ya shafi wasu sassan kasar nan ba.
Ibrahim ya fadi haka ne da ya ke ba mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo bayanai kan shirin da rundunar tayi da wanda take yi zuwa yanzu.
Shirye-Shiryen sun hada da:
1 – Za mu tura jami’an mu ko ina a fadin kasar nan.
2 – Mu na tattataunawa da gwamnatocin jihohi minti-minti domin samun bayanai akan halin tsaron jihohin su ce ciki.
3 – Muna kokarin ganawa da ‘yan siyasa don ganin sun lallashi magoya bayan su da jama’a domin ganin rikici bai tashi a wasu sassan kasar nan ba musamman a yankin Kudu Maso Gabas.