Hanyoyi 5 da PDP za ta bi don kwada APC da kasa a zaben 2019 – Goodluck Jonathan

0

Ganin yadda zaben 2019 ke kara matsowa, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan wanda ya sha kaye a zaben 2015, ya bayyana wasu fahamomi da lakanonin yadda jam’iyyar ta su za ta sake cin zabe a 2019. Jonathan ya bayar da wannan fahamin ne yayin da tsoffin kakakin majalisun jihohin kasar nan da a ka yi a zamanin PDP su ka kai masa ziyara a Abuja.

Ga wasu daga cikin lakanoni da fahamin nan daga bakin Jonathan, wanda a baya bai cika magana ba.

1 – Jam’iyyar PDP sai ta inganta tsarin deliget tun daga zabukan fidda gwanin kananan hukumomi har ya zuwa zabukan jihohi.

2 – Babbar matsalar PDP ta hada har da irin yadda jam’iyyar ke zaben ‘yan takara da kuma shugabanni a gwamnatin tarayya.

3 – A fito da tsari yadda ba wanda ya isa ya juya akala ko ra’ayin deliget masu zaben fidda gwani ba.

4 – A tabbatar duk wanda ya taba yin gwamna, minista, ko dan majalisa na jiha ko tarayya ko sanata, to a zabe su a cikin deliget masu zaben fidda gwani.

5 – Kada mu rinka dogara da yi wa talakawa dan hasafin cin abinci. Mu fadada hanyoyin jawo jama’a sosai.

Taron Gangamin jam’iyyar PDP mai zuwa ya tabbatar da ya gyara duk wasu dokokin jam’iyyar masu kawo mana matsala.

Hakan zai sa duk wanda ya fadi zaben fidda gwani zai hakura kuma ya taimaki wanda ya yi nasara, ba wai ya fusata ya koma wata jam’iyya ko ya zauna cikin PDP, amma yay i mata zagon kasa ba.

Nan ba da dadewa ba zan bayyana gaskiyar dalilin da ya sa PDP ta fadi zabe. Kun san ita siyasa sai da iya taku.

Akwai abin da ko da ka fadi a yanzu duk gaskiyar ka, ba za a fahimce ka ba. Amma bayan shekaru kamar hudu ko biyar za ka iya fitowa ka fada sannan wadanda ba za su saurare ka ba, su ne za su fi ba ka aron kunnuwan su, su saurare ka.

Share.

game da Author