Shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Calaba jihar Cross-Rivers, Thomas Agan ya ce sama da kashi 90 bisa 100 na mutuwan marasa lafiya a asibitocin kasarnan na da nasaba da sakacin ma’aikatan asibiti da likitoci.
Ya ce duk da irin horan da ake ba ma’aikatan asibiti kan yadda zasu ba mara lafiya kula bai hana su nuna halin ko in kula ga marasa lafiya a asibitocin mu.
Thomas Agan ya ce idan ba ma’aikatan kiwon lafiya sun fara daraja ran marasa lafiya ba kamar nasu ko na ‘yan uwan su ba ba za a rabu da wannan matsalar na mutuwan marasa lafiya da ake samu ba.
Ya ce kamata ya yi asibiti ta zama wurin da ake tausaya wa marasa lafiya ko da shi talakane ba wajen da zai zamo inda kuma zai rasa rayuwarsa.
Bayan haka Thomas Agan ya koka akan yadda sai likitoci sun tafi yajin aiki kafin su sami biayan bukatunsa ko kuma abin da suke nema wajen gwamnati.
Discussion about this post