Yawan Alhazan da su ka fito daga Najeriya da su ka rasa rayukan su a yayin ayyukan Hajjin bana ya kai 14.
Babban jami’in tawagar likitoci masu kula da lafiyar Mahajjatan Najeriya, Ibrahim Kana ne bayyana haka yayin ganawa da manema labarai, ranar Litinin a birnin Makka. Kana ya ce a cikin su kuwa har da, jami’in Hukumar Alhazai ta Kasa guda daya.
” Zuwa yau Litinin, 4 ga Satumba, 2017, mun rasa Alhazai 14. Bakwai sun rasu kafin Arafat, bakwai kuma bayan Atafat.
“Wadanda su ka rasu kafin Arafat, biyu daga cikin su daga jihar Kaduna, daya daga Yobe, Kogi, Kebbi da Katsina kowanen su. Sai kuma bakwai da aka rasa bayan Arafat sun fito daga: Jihohin Kano, wadda ta rasu Alhazai biyu, sai Osun, FCT, Zamfara da kuma Katsina.
” Muna kuma shaida muku cewa a cikin wadanda aka rasa akwai jami’in Hukumar Alhazai guda daya.”
Kana ya kara da cewa an yi da matsanancin zafi a Mina da kuma yayin Arafat a wannan shekarar, har ya kara tabbatar da cewa tsananin zafin rana sai da ya kai ma’aunin digiri 40%.
“Wannan ya haifar da zafi, shidewar numfashi, rashin ruwa a jikin jama’a da sauran wahalhalu.”
Dalili kenan inji Kana aka samu rasuwar Alhazan Najeriya guda biyu a Mina.