Jami’in hulda da jama’a na hukumar Alhazai na jihar Kano Nuhu Badamasi ya sanar da rasuwar wasu mahajjata 2 daga jihar.
Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai a garin Makka, Nuhu ya ce mutanen sun rasu ne bayan kammala ayyukansu na Hajji.
Ya ce mahajjatan da suka riga mu gidan gaskiya sun fito daga kananan hukumomin Dala ne da Doguwa.
Daga karshe ya ce mahajjatan jihar za su far dawowa ne daga ranar 5 ga watan Satumba.