HAJJIN BANA: An daure wani dan Najeriya da aka kama da laifin sata a Saudiyya

1

Kotun a kasar Saudiyya ta daure wani mahajjaci dan Najeriya daga karamar hukumar Goronyo jihar Sokoto har na tsawon watani uku.

Kotun ta yanke masa hukuncin hakan ne bayan kama shi da laifin satan jakar wani mahajjaci dan uwarsa ya saci a masallacin Makkah ranar Juma’a.

Sakataren karamar hukumar Goronyo Lawal Yar-tsakuwa ya tabbatar da hakan inda ya bayyana cewa bayan Mamman Kwakwazo ya tsinci jakan sai ya ki fadi hakan wa jami’an tsaron dake wurin.

‘‘Gaddama ne ya barke tsakanin Mamman Kwakwazo da mai jakan domin mai jakan ya gane jakarsa sannan shi kuma Mamman yace jakarsa ce’’.

Bayan haka Lawal Yar-tsakuwa ya ce an kama Mamman a ranar Juma’a, kotu kuma ta yanke masa hukuncin zama a gidan yari har na tsawan watanni uku.

Kasar Saudiyya ta ce ba za ta amince Mamman ya sake shigowa kasar ba sai bayan shekara biyar.

Share.

game da Author