HADURRA: Najeriya ta rasa mutane 423 a cikin watan Yuli -Cewar Hukumar Kiyaye Hadurra

0

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa, FRSC, ta bayyana cewa a kullum a cikin watan Yuli, akalla mutane 13 su ka rika mutuwa a kan titinan kasar nan.

Wannan bayanin ya fito ne daga cikin wata mujalla da hukumar ke wallafawa mai a wata-wata. Mujallar ta yi dalla-dalla cewa mutane 423 su ka mutu ta hanyar hadurra, 2339 su ka ji ciwo, yayin da aka samu yawaitar hadurra har 768.

“An samu karin yawaitar hadurra a cikin Yuli, fiye da na cikin watan Yuli. A Yuli, mutane 301 su ka mutu, wato an samu karin 122 sama da Yuni.

Har ila yau, rahoton ya bayyana cewa hadarin da aka yi na watan Yuni 2157. shi ma bai kai na watan Yuli ba,

Yawan hadurran watan Yuni 738 ne, bai kai 768 ba da su ka afku a cikin Yuli. Abuja ne aka fi samun yawaitar Hadurra, yayin da Jihar Kaduna ke bi mata a jiha ta biyu.

Share.

game da Author