Gwamnoni 5 daga Arewacin kasar nan sun kai ziyara yankunan Kudu-maso-gabas da Kudu-maso-kudu domin kai ziyarar kwanaki biyu, da nufin kara jaddada dorewa zaman lafiya a kasar nan.
A cikin wata takarda da kakakin gwamnan Sokoto, Imam Imam ya sa wa hannu, ya ce gwamnonin sun tafi ziyarar ne a bisa jagorancin shugaban gwamnonin Arewa, Kashim Shettima.
Sauran gwamnonin sun hada da na Katsina, Aminu Masari, Aminu Tambuwal na Sokoto, Abubakar Bagudu na Kebbi da kuma Simon Lalong na Filato.
Gwamnonin 5 za su tattauna da gwamnonin Rivers, Abia da na Jihar Imo.
Haka nan kuma Imam ya ce za su gana da sarakunan gargajiya da shugabannin addini kuma za su gana da ‘yan Arewa mazauna yankunan.
Sun kuma kara jaddada wa ‘yan Nijeriya cewa kowa na da ‘yancin zama a kowane yanki na kasar nan.
Ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na sane da wannan ziyara da za su kai, kuma ya karfafa su.