Gwamnatin Tarayya za ta samar wa manoma buhuhunan taki miliyan 50 kafin karshen 2017

0

Kakakin fadar shugaban kasa, Garba Shehu ya ce gwamnatin tarayya za ta samar wa manoma buhunan taki miliyan 50 kafin karshen wannan shekara.

Garba Shehu ya fadi haka ne a shirin Hannu da Yawa da a keyi duk Asabar a gidan rediyon tarayya na Kaduna.

Ya ce bayan haka gwamnati za ta kara yawan kamfanonin sarrafa taki daga 11 zuwa 18, inda hakan zai sa a samar wa matasa aikin yi a kasar.

Bayan haka kuma ya ce dalilin irin kokarin da gwamnatin tarayya tayi a harkar noma ya sa an sami ci gaba da saukin abinci a kasar yanzu.

” Da buhun masara ya kan kai 20,000 amma yanzu bai wuce 10,000 ba.

Share.

game da Author