Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin a gaggauta binciken Hukumar Shirya Jarabawar shiga jami’a, wato JAMB da kuma Hukumar NIMASA.
Hakan ya biyo bayan kakarin da aka ga Shugaban JAMB na yanzu ya yi inda a cikin shekara daya ya tara kudin shiga har naira bilyan 5, yayin da kuma ya ke kan hanyar kawo sauran balas na naira bilyan 3.
Wannan kokarin ne ya tashi tsohon ballin shugabannin da suka gudana, inda Ministar Kudi Kemi Adeosun ta ce ba su taba tara sama da naira miliyan 3 kacal a shekara ba.
Wannan tonon silili da aka yi wa tsoffin shugabannin JAMB, an yi shi ne jiya Laraba a fadar Shugaban Kasa wurin taron Majalisar Zartaswa.
Idan ba a manta ba, cikin watan Yuli ne Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa ya tara naira bilyan 5, kudin da hukumar ba ta taba tarawa shekaru 40 baya ba.
Dalili kenan Ministar ta ce ya zama dole a binciki shugabannin hukumar da aka yi kafin Ishaq Oloyede.
Haka kuma gwamnatin tarayya ta ce za ta binciki Hukumar Kula Da Tsaron Sifirin Tashoshin Jiragen Ruwa, wato NIMASA.