Gwamnatin jihar Sokoto ta mai da makarantun Islamiyya 4000 zuwa Islamiyya da Boko.
Kwamishinan ilimin firamare da sakandare na jihar Jabbi Kalgo ya ce gwamnati ta yi haka ne don ta inganta karatun yara a jihar da kuma kara wa iyaye karfin guiwar saka ya’yansu a makarantun.
Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad ne ya jagoranci tawagar jami’an gwamnati da suka ziyarci makarantun.
Kalgo ya ce gwamnatin jihar ta samu taimako da hadin guiwar UNICEF domin samun nasara kan hakan.
Sannan ya ce gwamnati za ta ci gaba da yin hakan ga wasu makarantu a jihar.
Discussion about this post