Gwamnatin Jihar Neja ta biya wa Dauda Mohammed kudin Magani

0

Mai taimaka wa gwamnan jihar Neja kan harka yadda labarai Jide Oritunsi ya ce gwamnatin jihar ta bada Naira miliyan 13 don a biyan kudin asibitin tsohon shugaban kungiyan dalibai na kasa Dauda Mohammed.

Ya fadi haka ne wa kamfanin dillancin labaran Najeriya yau Alhamis a Minna.

Ya bayyana cewa Dauda Mohammed na fama da cutar dajin dake kama huhu wanda ake kira da ‘liver cirrhosis’ kuma yana bukatan kudi don zuwa asibiti a kasar India.

Jinkirta samar da kudin yasa kungiyar dalibai yin zanga- zangan lumana donnjawo hankalin gwamnati akan haka.

Jide ya sanarwa daliban a wancan lokaci cewa gwamnati bata ki samar da kudin wai don ba ta son yin kana ne ba.

Share.

game da Author