Furucin da Saraki yayi kan haramta kungiyar IPOB, Burgar siyasa ce da neman suna kawai – Ado Doguwa

1

Bulalar Majalisar Wakilai , Hon. Alhassan Doguwa, ya soki Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, dangane da furucin da ya yi cewa ba daidai ba ne hukumar tsaron sojoji ta kasar nan ta kira ‘yan Kungiyar neman kafa Biafra da sunan ‘yan ta’adda, domin basu da ikon yin haka.

Doguwa, wanda dan majalisar tarayya ne mai wakiltar Karamar Hukumar Doguwa daga Kano, kuma dan jam’iyya daya da Sanata Saraki, ya ce furucin Saraki ‘‘siyasa da ice kawai.”

“Ni ina ganin furucin da Saraki ya yi kawai kasassabar ‘yan siyasa ce wadda kuma za ta janyo masa bakin jini.

Doguwa ya ce idan aka yi la’akari da irin hari da kisan da kungiyar ta IPOB ta yi kan jama’a da dama a Kudu-maso-Gabas da kuma kokarin da gwamnonin Arewa su ka yi domin hana daukar fansa a Arewacin kasar nan, to kalaman Sanata Saraki bai ma kamata ya furta su ba.

“Na tabbata wannan ra’ayin sa ne kawai ya furta, wanda kuma na yi amanna da cewa kwata-kwata bai dace ba a halin da ake ciki.

“Ka ga ni kuma a nawa ra’ayi na shi ne, sojojin kasar nan su na yin bakin kokarin su wajen tabbatar da karin hada kai a Najeriya.

“Ku dai duba ku gani, hatta gwamnonin Kudu-maso-Gabas sun haramta kungiyar ta Biafra. Don haka bai dace Saraki ya fito ya na babatun sukar wadanda su ka haramta kungiyar ba.

Share.

game da Author