Fayose burga kawai yake yi amma PDP ba za ta tsayar da wani dan kudu takarar shugaban kasa ba, 2019 na Arewa ne – Jam’iyyar PDP

0

Jam’iyyar PDP ta umarci Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose da ya manta da mafarkin tsayawa takarar shugabancin kasar nan a 2019, da ya ke yi, domin a cewar ta, bata wa kan sa lokaci kawai zai yi.

Sakataren Yada Labaran jam’iyyar ne, Dayo Adeyeye ya bayyana haka a cikin wani jawabi da ya sa wa hannu a yau Laraba. Ya na mai cewa ai tuni jam’iyyar ta rattaba cewa dan takarar PDP a zaben 2019 daga Arewa zai fito.

Fayose dai tun a ranar Alhamis da ta gabata ne ya bayyana aniyar sa ta neman tsayawa takara a karkashin PDP a 2019.

Ya yi bayanin ne ta bakin kakakin yada labaran sa.

Sai dai kuma PDP ta ce Fayose zai iya tsayawa takarar shugaban jam’iyyar PDP na kasa tunda wannan mukamin an bar wa ‘yan yankin kudancin Najeriya shi.

Sauran wadanda ake da yakinin za su tsaya takarar shugabancin jam’iyyar PDP daga kudu, sun hada da tsohon gwamnan Ondo, Olabode George, tsohon gwmnan Ogun Gbenga Daniel, dukkan su kamar Fayose din, duk ‘yan yankin Kudu-maso-yamma ne, yankin da zai samar da shugabanjam’iyya na PDP.

“Wannan batu dai a fili ya ke, taron Gangami na Kasa, ai shi ne jam’iyya, kuma PDP a wurin wannan taro ta amince cewa daga Arewa za a tsayar da dan takara a 2019.

“A matsayin Fayose na gwamna, ya je taron gangamin, kuma yana sane da haka. Ashe kenan bai ma kamata ya fito ya na wani azarbabin neman tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin PDP ba.

“Idan manyan jam’iyya irin su Fayose na fitowa su na irin haka, to me kuma za mu yi tsammani daga na kasa da mu?”

Share.

game da Author