El-Rufai ya yi ta’aziyya ga iyalan Marigayi Kasimu Yero

0

Dubban Masoya, yan uwa da abokan arziki ne suka halarci jana’izan marigayi Kasimu Yero a Kaduna.

Bayan haka gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da wasu jami’an gwamnati da ya hada da sirikin marigayin Honarabul Yusuf Zailani na daga cikin mutane na farko da suka kai ziyarar gaisuwa ga iyalan mamacin.

Marigayi Kasimu Yero shahararren dan wasan fina-finan Hausa ne wanda aka fi sani da yin fice a shirin fim din Magana Jari ce.

Kamar yadda Yakubu Aliyu ya sanar da PREMIUM TIMES, Kasimu Yero ya rasu ne a gidansa da ke rukunin gidaje na Marafa dake Kaduna.

Share.

game da Author