A yau ne gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya bude kamfanin sarrafa abincin kaji wanda kamfanin ‘Sunseed’ ta gina a Zariya, jihar Kaduna.
Yayin da yake yin jawabinsa a wajen kaddamarwan El-Rufa’I ya ce gwamantin jihar Kaduna za ta ci gaba da kirkiro hanyoyin samar da aikin yi wa matasan jihar musamman a fannin noma da hako ma’adanai.
Ya ce bunkasa aiyukkan noma da hako ma’adanai a jihar Kaduna zai taimaka wa jihar samun cin gashin kanta batare da ta dogara da kaso daga gwamnatin tarayya ba.
Ya ce gwamantinsa na kokarin ganin yadda za su jawo masu zuba jari a fannin noma a jihar musamman yadda aka san manoman jihar da noman wake, cita, masara,tumatir da sauransu.
“Za mu farfado da kamfanin sarrafa abincin dake Ikara, Sannan za mu karfafa manoman jihar wajen noma shinkafa, alkama da waken da ake ci a kasar Sin domin a fara fitar da su.”
Bayan haka gwaman jihar Kaduna ya jinjinawa kamfanin ‘Sunseed’ da gina asibitin da ke daukan yawan gadaje 15 wa mazauna garin Zariya.
Mai martaba sarkin Zazzau ya ce gina kamfanin sarrafa abincin kaji a Zariya zai samar wa mutane da dama aikin yi.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dawo da shirin siyan amfanin gona wajen manoma domin tallafawa manoman jihar.