Duk da nada sabon shugaba, ma’aikatan hukumar NAFDAC sun ce yajin aiki na nan daram

0

Ma’aikatan hukumar NAFDAC sun ce ba za su dakatar da yajin aikin da suka shiga ba duk da cewa an nada sabon shugaban hukumar.

Idan ba a manta ba ma’aikatan hukumar NAFDAC sun shiga yajin aiki ne saboda tsohuwar shugaban hukumar Yetunde Oni ta ki sauka daga kujeran sugabancin hukumar duk da cewa shekarun aikinta sun cika sannan da rashin gamsuwa da basu yi ba kan yadda ake tafiyar da shugabanci a hukumar musamman wanda ya shafi Albashi.

A yanayin da ake ciki dai Yetunde Oni ta sauka sannan Ademola Mogbojuri darektan horo da bincike na hukumar na reshen jihar Kaduna ya maya gurbinta.

Shugaban kungiyar ma’aikatan hukumar Idu Isua yace za su gudanar da yajin aikin yanzu da tushe musamman yanzu da suka sami sabon sugaba.

Share.

game da Author