Duk da dawowar Ronaldo, Madrid ta kwashi kashinta a hannu

0

Kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid ta kwashi kashinta a hannu bayan kayi da tasha a hannu takwaranta Real Betis a filin ta na Benabau dake Madrid.

Abin dai kamar almara domin ana bugawane kamar ba ayi ba. Madrid na ta fizge-fizge kamar za su yi wa Betis ruwan gwal-gwalai ashe garinsu da nisa. Minti uku da kammala wasan, dan wasan Betis ya ko makala musu kwallo daya mai ban haushi.

Kafin kace kwabo fili ya rude da ihu inda magoya bayan Madrid ko sai suka fara tashi daya bayan daya suna kaucewa.

Yanzu dai madrid ne ta 7 a tebur, tana da maki 8 cikin wasanni 5 da aka buga zuwa yanzu.

Barcelona ce ke kan gaba da maki 15 cikin wasanni 5.

Ga yadda sauran wasannin suka kaya:

Barcelona 6 – 1 Eibar

Athletic Bilbao 1 – 2 Atletico Madrid

Leganes 0 – 0 Girona

Deportivo La Coruna 1 – 0 Alaves

Real Madrid 0 – 1 Real Betis

Sevilla 1 – 0 Las Palmas

Valencia 5 – 0 Malaga

Share.

game da Author