Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana cewa za ta fara sabon shirin yi wa Sanata Dino Melaye kiranye a ranar Litinin mai zuwa.
A cikin wata takarda wadda Kwamishina na Tarayya, Muhammad Haruna ya sa wa hannu a yau Talata, sanarwar ta ce a ranar 18 Ga Satumba hukumar za ta bayyana sabbin ranakun da za ta fara akin yi wa Sanatan na Kogi ta Yamma kiranye.
“Idan ba a manta ba, INEC ta bi umarnin kotu tun a ranar 6 Ga Yuli, 2017, inda ta dakatar da dukkan wasu tsare-tsaren da ta ke yi na yi wa Dino kiranye.
“To a jiya 11 Ga Satumba, 2017, kotu ta kawar da duk wani tsaiko, ta hanyar yanke hukunci cewa babu dalilin da zai sa a hana INEC aiwatar da kiranyen.
“Don haka, kamar yadda kundin dokar kasa da kundin dokokin Hukumar Zabe da kuma ka’idoji da sharuddan hukumar su ka gindaya, INEC za ta bi sabon umarnin kotu na ci gaba da yi wa sanatan kiranye.
“A kan haka, hukumar na sanarwa cewa a ranar Litinin, 18 Ga Satumba, 2017 za ta sake tsara sabon jadawalin ranakun da za a gudanar da kiranyen.