Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sanar wa manema labarai cewa babatun da ministan mata Aisha Alhassan tayi cewa ko Buhari ya fito ba za ta mara masa baya ba a 2019, ya ce Aisha ta fadi ra’ayin ta ne kawai amma da bata taba yin Buhari ba.
El-Rufai ya ce dama can ita ba masoyiyar Buhari bane, Kauna ce kawai ya sa Buhari ya yi mata minista amma ba wai don da yawa ya’yan jam’iyyar suna son haka ba.
“Muna da wata kungiyar masoya Buhari wanda ya hada da wasu gwamnoni da ministoci kuma tuni mun fara shirye-shiryen ganin Buhari ya fito takara a 2019.”
” Maganganun da Aisha tayi bai bani mamaki ba ko kadan domin da ma can ba ta tare da Buhari, ita Atiku ta keyi. Ko bayan dayawa daga cikin ‘yan siyasan jam’iyyar APC sun nuna kada ayi mata minista, Buhari shi kadai ne ya ce zai yi mata kuma yayi mata ministan. Amma ta na da ikon fadin ra’ayinta.”
El-Rufai ya fadi haka bayan ganawa da yayi da shugaban kasa a fadar gwamnati.