Wasu sojoji sun harbe wasu manoma uku yayin da suke hanyar zuwa gonar su a karamar hukumar Madagali jihar Adamawa.
Mazauna kauyen Madagali sun ce sojojin sun harbe Yohanna Anarayu tare da kannansa biyu akan babur yayin da suke wucewa ne ta kauyen.
” Sojojin sun harbe manoman ne saboda karya dokar yin amfani da babura a kauyen da sojoji suka kafa shekaru uku da suka wuce.
“Nan da nan sai suka fara harbin babur din inda Yohanna da Kannan sa suka yada babur din suka tsere.”
” Duk da hakan sojojin basu daina harbinsu ba har sai da su kaga sun mutu.”
Shugaban karamar hukumar Madagali Yusuf Muhammad yayin da yake tabbatar da hakan wa manema labarai ya ce sojojin sun kafa dokar hana amfani da babura saboda sun sami labarin cewa wasu ‘yan garin na taimakawa Boko Haram.
Ya kuma kara da cewa mutanen kauyen sun fara amfani da baburan su ne bayan zaman lafiya da aka samu a yankin.