Dalilan da ya sa ma’aikatan hukumar NAFDAC suka shiga yajin aiki

0

Kungiyar ma’aikatan hukumar NAFDAC ta shiga yajin aikin daga yau 22 ga watan Satumba.

Kungiyar ta ce ta shiga yajin aikin ne bayan gazawa da ma’aikatar tayi na gyara albashinsu da tayi alkawari tun shekarar 2013.

Shugaban kungiyar Idu Isua yace wannan yajin aikin ba shine karo na farko da ma’aikatan hukumar suka taba yi ba.

‘‘Mun taba zuwa irin wannan yajin aiki shekaru uku da suka wuce amma saboda da alkawarin gyara albashin da ma’aikatan ta dauka ya sa muka dakatar da yajin aikin a wancan lokacin.

Bayan haka shugaban kungiyar ma’aikatan ya ce shugaban hukumar NAFDAC din Yetunde Oni ya kamata ta sauka daga kujeran ta na shugabancin hukumar domin ta kai adadin yawan shekarun da ya kamata ta yi tana aikin gwamnati.

” Yetunde Oni ta kai shekaru 60 tana aikin gwamnati wanda bisa ga dokokin ma’aikatan gwamnati bai kamata ba ta ajiye aiki ba har yanzu.”

Share.

game da Author