Wani likitan mata Chris Abumchi ya ce Najeriya ce ta uku cikin jerin kasashen duniya da ake haihuwar jarirai bakwaini.
Kamar yadda ya sanar Chris ya ce bincike ya nuna cewa matsalar haihuwar bakwaini ya shafi kasashen duniya ne baki daya inda hakan ya nuna cewa cikin kowani haihuwa 10 ana samun bakwai ni.
“Bakwaini shine idan mace ta haifi yaron da wasu bangarorin jikinsa basu gama haduwa ba domin an haife shi kafin watanin hahuwan shi su cika.”
Dalilai 6 da ke sa mace ta haifi da’ Bakwaini;
1. Zukar Taba sigarin.
2. Mai dauke da Cutar siga (diabeties) ta Uwa ko ta uba.
3. Amfani da magungunan da wasu mata masu ciki ke yi batare da izinin likita ba.
4. Shan giya.
5. Rashin cin abincin da ya kamata.
6. Yawan rashin samun natsuwa da kwanciyar hankali ga mai ciki.
Ya kuma yi kira ga mata masu ciki cewa da zaran sun fara samun ciwon ciki ko kuma zuban jini da su gaggauta zuwa asibiti domin ganin likita sannan su dinga zuwa asibiti a akai-akai domin samun bayanai kan hanyoyin gujewa haiho bakwaini.