Daliban jami’o’in Najeriya sun yi murna da janye yajin aiki da ASUU ta yi

0

Daliban jami’o’in Najeriya da sun yi murna matuka da janye yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’I na kasa ASUU ta yi.

Kungiyar ASUU ta janye yajin aikin ne ranar Litini bayan awoyi da tayi suna tattauna wa ministan kwadugo da jami’an ma’aikatan Ilimi.

Shugaban kungiyan daliban jami’o’in Chinonso Obasi ya jinjina wa Kungiyar ASUU da na kwadugo da suka samu daidaituwa kan alkawurran da suka dauka.

Ya ce dakatar da yajin aikin ya taimaka wa iyaye da dalibai.

Ya kuma yi kira ga gwamnati tarayya da ta daure ta cika alkawurran da ta dauka.

Share.

game da Author