Rudani ya barke a wata Unguwa dake garin Abuja inda aka zargi wani matashi mai suna Usman da sace ma wani yaro gabansa daga shan hannu da suka yi.
Wannan abu dai ya faru ne a Unguwan Kurudu da ke garin Abuja.
Wanda a ka sace wa gaban na sa mai suna Salvation ya bayyana wa gidan jaridar PREMIUM TIMES cewa da misalin karfe 7:45 na yamman jiya, a daidai yana kokarin rufe shagon wansa don ya kalli wasan kwallon kafa sai Usman ya rokeshi da ya nuna masa inda gidan karuwai yake a unguwar.
“Bayan da na nuna masa gidan sai muka sha hannu nan da nan sai na ji daban a jikina.”
Laluba jikinsa da Salvation zai yi sai ya ji gabansa ya bace. Nan da nan ya sa ihun barawo mutane suka taru suka kama Usman.
Wani wanda abin ya faru a idon sa ya ce sojoji ne suka kwaci Usman daga hunnu mutane domin da an kashe shi.
Shi kuma Usman ya karyata kazafin da aka yi masa domin ya ce ya shigo anguwar ne don neman gidan karuwai.
“Kafin na ankara sai naga mutane a kaina suna dukana wai na sace masa gaban sa.”
Da sojojin suka sa baki a maganan sai Usaman ya dawo wa Salvation da gabansa.
Wani cikin mutanen da suka taru a wurin ya bada shawaran cewa Salvation ya shiga gidan karuwan domin ya tabbatar da ingancin gabansa.
Bayan dan wani lokaci sai Salvation ya fito yana murmushi saboda sanun tabbacin gabansa.
Discussion about this post