DA ALAMA AN SHIRYA: Hunkuyi da El-Rufai sun halarci taron APC a Kaduna

0

Duk da rade-radin da ake ta yadawa cewa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da Sanata Suleiman Hunkuyi yau dai abin kamar ya canza salo domin da Sanata Sule da shi kanshi gwamna El-Rufai sun hadu a dakin taro na Umaru Musa Yar’Adua dake Kaduna a taron jam’iyyar APC na jihar yau.

Duk da cewa Hunkuyi ya ce idan har gwamnan jihar bai gyara yadda yake juya jam’iyyar ba zai yi masa adawa a zabe mai zuwa. Yau dai ta nuna lallai za a shirya domin sai gasu su biyun da sauran ya’yan jam’iyyar tare a taron.

Ko da yake shi kadai ne cikin sauran wadanda ke da matsala da jam’iyyar a jihar, sanata Shehu Sani da sauran magoya bayan jam’iyyar APC Akida da restoration.

Da alama dai za a ci gaba da tafiya tare sannan jam’iyyar a jiha na kokarin dinne barakar da ke jam’iyyar.

Share.

game da Author