Cutar Kwalara ya addabi mata musamman mazauna sansanin ‘yan gudun hijira – UNFPA

0

Wani jami’in asusun UNFPA Homsuk Swomen ya koka kan yadda cutar kwalara ke saka mata cikin halin kakanikayi a yankin arewa maso gabacin Najeriya.

Homsuk Swomen yace bisa ga binciken Asusun UNFPA ya nuna cewa saboda aiyukkan Boko Haram miliyan 1.7 na mutanen yankin sun zama ‘yan gudun hijjira wanda hakan na daya daga cikin dalilan da ke hana su samun ingantaciyyar kiwon lafiya.

UNFPA ta ce a watan Agusta kawai mutane da dama a yankin sun kamu da cutar kwalar sannan mafi yawan su mata ne masu ciki.

‘‘Idan mai ciki ta kamu da cutar kwalara da ita da dan dake cikinta na cikin matsalar wanda ke yin ajalinsu, ko ya sa macen ta haiho bakwaini da sauransu.

Ya kuma kara da cewa kamata ya yi a wayar da kan mata domin su ne cutar ta fi kamawa saboda yawan aiki da ruwa da suke yi.

Bayan haka shugaban ma’aikatan kiwon lafiya na jihar Borno Mohammed Ghuluze ya ce yaduwar cutar ta ragu saboda aiyukkan da ma’aikatarsu tare da wasu kungiyoyin bada tallafi suka yi.

‘‘Mun kafa wuraren da mutanen da suka kamu da cutar za su iya samun kula sannan ma’aikatan kiwon lafiya na bada kula na matakin faro wa mutane ta hanyar bi gida-gida’’.

Share.

game da Author