Cutar Farar Massasara ta bullo a jihar Kwara.

0

Ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar da bullowar cutar Farar Massasara a jihar Kwara

Ma’aikatar ta ce an gano cutar ne ranar 12 ga watan Satumba bayan babbar asibitin koyarwa na jihar Legas ta gudanar da bincike a jikin wata yarinya.

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya wanda ya hada da ma’aikatan kungiyar WHO, hukumar NCDC, hukumar NPHCDA sun hada guiwa domin gudanar da bincike akan cutar a kauyen da cutar ta bullo da sauran kauyukan da ke kusa da garin.

Ya kuma ce sun kafa kwamitin da za ta nemo hanyoyin da za a bi domin hana yaduwar cutar.

Isaac Adewole ya ce alamomin cutar sun hada da zazzabi, ciwon kai, yawan gajiya da sauransu.

Ya ce iyaye za su iya samun allurar cutar wa ‘ya’yansu a asibitoci da wuraren da ake bada allurar rigakafi kyauta.

Bayan haka Isaac Adewole ya yi kira ga mutanen jihar da su tabbata sun tsaftace muhallinsu musamman wuraren da ruwa ke yawan kwanciya.

Ya shawarci ma’aikatan kiwon lafiya da ke kula da wadanda suka kamu da cutar da su kare kansu domin hana yaduwar cutar.

Share.

game da Author