Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya koma kasar Britaniya daga kasar Amurka bayan halartar taron Majalisar Dinkin Duniya.
Gwamnonin jihohin Zamfara, Ebonyi da Ondo na daga cikin tawagar shugaban kasan.
Ko da yake babu wani bayani akan wucewa kasar Britaniya da yayi daga fadar shugaban kasar, kakakin fadar shugaban kasar, Garba shehu yace shima ba shi da masaniya akan tafiyar shugaban kasan domin shi yana Najeriya ne yanzu haka.