Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta tsayar da shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Nasir El-Rufai yan takaran ta a zabe mai zuwa.
Jam’iyyar ta sanar da haka ne a taron gangami na jam’iyyar da tayi jiya a garin Kaduna.
Taron ya sami halartar jigajigan jam’iyyar a jihar da ya hada da gwamnan jihar Nasir El-Rufai, Sanata mai wakiltan Kaduna ta Arewa, Suleiman Hunkuyi, mai ba gwamnan jihar shawara akan harkar siyasa, Uba Sani da sauran yayan jam’iyyar.
Da yake nashi jawabin a taron shugaban jam’iyyar Shuaibu Idris, y ace an shirya wannan taro ne domin a dinke barakar da ke jam’iyyar a jihar sannan a tattauna akan hanyoyin da za a bi wajen samun nasarar jam’iyyar a jihar da kasa baki daya.
Sannan kuma y ace jam’iyyar ba za ta yi kas-kasa ba wajen hukunta duk wanda ya karya dokar jam’iyyar ko shi waye.
Gwamnan Kaduna, El-Rufai, yayi wa jam’iyyar bayani akan ayyukan da gwamnatin jihar ke yi yanzu haka sannan kuma yayi wa mutanen jihar alkawarin samar musu da ababen more rayuwa kamar yadda jam’iyyar ta yi alkawari.
Sanata Suleiman Hunkuyi wanda yayi zuwan bazata wurin taron y ace dole ne jam’iyyar ta hada karfi da karfe wajen ganin itace ta sami nasara a zaben 2019.
Discussion about this post