Buhari, APC sun yi watsi dani duk da muhimmiyar rawar da na taka – Atiku Abubakar

0

Tshohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce tun bayan samun nasarar jam’iyyar APC Buhari da gwamnatinsa suka yi watsi dashi kamar ba da shi aka wahala a wancan lokacin ba.

Da yake hira da gidan jaridar VOA, Atiku ya ce bayan sun taimakawa jam’iyyar APC da karfinsu da kuma dukiyoyinsu watsi da su ne sakamakon abin da suka samu daga gwamnatin Buhari.

“ Bari in gaya muku gaskiya, ni dan jam’iyyar APC ne, tare da ni akayi komai domin samun nasara a zaben 2015.”

“ Tun da aka kafa gwamnati, ba a taba ko tuntuba ta ba ko don shawara ko makamancin haka. Amma ni na tsaya a inda nake. Sun yi amfani da kudaden mu domin kai wa inda suke yanzu amma yanzu sun yi watsi da mu.”

Yace duk da cewa an sami nasarori a yaki da Boko Haram, ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba.

“ An sami nasarori amma fa har yanzu abin kamar da wuya domin ana ta kashe mana mutane a kauyukan jihohin Yobe da Barno.

“ Abin yana ba ni mamaki ace wai Najeriya ta kasa kakkabe Boko Haram shekaru biyar wanda bai kai yakin basasa ba da cikin watanni 30 an gama.

Ya ce game da yaki da cin hanci da rashawa, gwamnatin ba ta yi wani abin azo a gani tunda idan ka tambaya mutum nawa ne aka gurfanar sannan aka yanke wa hukunci ko a ka daure, za ka ga ba kamar yadda a lokacin mulkin su da Obasanjo ba inda sun kwato kudade da ya kai Dala Biliyan 4.5 da ka sace a kasar nan.

Share.

game da Author