Boko Haram sun kashe limami da mutane 16 a Barno

0

Boko Haram sun kai wani mummunan hari inda su ka kashe wani limami da mutane hudu a kauyen Kutumari da ke cikin Karamar Hukumar Magumeri.

Jami’an Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Barno ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai, NAN cewa an kai wannan hari ne a ranar Lahadi da ta gabata.

Ya ce hari na biyu wanda ya fi muni, shi ne wanda kungiyar ta sake kaiwa washegari Litinin a kauyen Mashemeri da ke cikin Karamar Hukumar Konduga.

Ishaku Victor ya ce a wannan harin wasu ‘yan kunar-bakin-wake ne su biyu, namiji da mace, su ka kai harin, inda a take mutane 13 su ka mutu, wasu 16 su ka ji munanan raunuka.

Share.

game da Author