BIAFRA: Mun kashe bakin tsanya – Cewar Buratai

1

Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa sun yi nasara a kan tsagerun Biafra, wadanda su ka nemi hana ruwa gudu a Yankin Kudu-maso-gabas.

Wannan jawabi ya fito ne a jiya Juma’a bayan da Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Tukur Burutai ya yi ziyarar zagayen gani da ido na irin atisayen da sojoji ke yi a yankin.

Kakakin rundunar Kanar Sagir Musa, ya ce a yanzu shiru ka ke ji a yankin, babu sauran wani dan ta’addar Biafra da ke gilmawa a fili, tamkar ruwa ya ci su.

“Amma kafin mu fafare su, har sojojin sa-kai su ka kafa, na rashin kunya masu kafa shinge kan titina subka karbar kudade ga masu wucewa.

” Sauran jami’an tsaro na ta’addanci da su ka kafa ma duk sun bace. Jama’a na ta walwalar su, hankali su kuma kwance.” Inji Sagir.

Tsagerun Biafra dai sun kara karfi ne bayan an bayar da belin shugaban su, Nnamdi Kanu, inda su ka rika tururuwa daga garuruwa daban-daban su ka hallara jihar Abia, mahaifar Nnamdi Kanu.

Kanu ya rika yin barazanar kashe shugaban kasa, haddasa fitina a kasa da kuma kone Najeriya. Bayan dakarun kan sa da ya kafa, ya kuma karya duk wasu ka’idojin belin da aka kafa masa.

Idan ba a manta ba, kafin dawowar sa Najeriya har a kama shi cikin Disamba, 2015, ya je kasashe, ciki har da Amurka inda ya nemi gudummawar makamai daga hannun kabilar Igbo mazauna kasashen.

A zaman yanzu dai ba wanda ya san inda Kanu ya ke. Ko da ya ke lauyan sa na zargin cewa ya na kyautata zaton sojoji sun kashe shi.

Share.

game da Author