Biafra: Majalisar Dattawa za ta zauna da hukumomin tsaro

0

Majalisar Dattawa za ta zauna da hukomomin tsaron kasar nan dangane da rikicin Biafra wanda ya faru cikin makon nan a yankin Kudu maso Gabas.

Shugaban Majalisar, Bukola Saraki ne ya bayyana haka a yau Lahadi. Ya ce za a tattauna ne domin ganin shawo kan yadda zaman lafiya zai dore, ganin yadda IPOB suka harzuka sojoji.

Kakakin yada labaran Saraki, Yusuf Olaniyonu ne ya raba wa manema labarai wannan bayani. Ya na mai cewa majalisar ta damu sosai ganin yadda kasar ta shiga wani halin da ta ce akwai dalilai na matsalar tattalin arziki da iya zama silar faruwar su.

Ya ce kasa ba za ta samu yarwar arziki ba matukar babu zaman lafiya a cikin ta.

Saraki ya rika kowane bangare da ya zauna lafiya tare da yarda, amintaka da kaunar zamamtakewa da juna.

Share.

game da Author