BIAFRA: Mai yiwuwa sojoji ‘sun damke Nnamdi Kanu, sun kashe shi – Cewar lauyan sa

0

Lauyan da ke kare dan taratsin neman kafa Biafra, Nnamdi Kanu, ya bayyana cewa hulda ta yanke tsakanin sa da Kanu tun daga ranar 14 Ga Satumba, ranar da sojoji su ka yi dirar mikiya a gidan sa.

Lauyan mai suna Ifeanyi Ejiofor, ya na magana ne yayin da ya ke bada bayanin shin ko Kanu ya gudu ne ya buya?

A cikin jawabin nasa, ya ce sojoji ne suka damke Nnamdi Kanu, kuma su ka tafi da shi. “Mai yiwuwa ma sun kashe shi.”

Rabon dai da a ga Kanu a waje cikin jama’a tun ranar 10 Ga Satumba, bayan magoya bayan sa sun yi arangama da sojoji.

Sai dai kuma a cikin wata wasika da ake rade-radin cewa Kanu ne ya rubuta ta, ya ce shi ba zai halarci zaman tattaunawa da gwamnonin Kudu-maso-gabas ba.

“Ni ba na ko tantama cewa surutan da ake yi wai Kanu ya gudu kasar waje, duk wani alaye ne da kuma yi wa jama’a bad-da-bami. Tun da mu ka yi waya ‘yan mintina kadan bayan an yi wa gidan dirar-mikiya, ban sake jin duriyar sa ba.”

“Idan sojoji su ka shiga gidan, na tabbata sai sun ci karo da shi. To ya kamata su fito ko dai su sanar idan an kashe Kanu yayin da ake harbe-harbe, ko kuma idan sun kame shi, sun tafi da shi.

“Ni dai a nawa zaton kawai sojoji sun kashe shi, amma sai su ke ta kokarin su cusa wa duniya hasashen cewa wai ya tsallake ya gudu daga Nijeriya. Ni dai abin da na ke nema shi ne, sojoji su fito min da Kanu, su daina karkatar mana da hankali cewa wai ya gudu.”

Yayin da ake rubuta labarin, kan kasa samun kakakin askarawan Najeriya, Sani Kukasheka, domin jin ta bakin sa. An yi masa sakon tes ta lambar wayar sa, amma har yanzu bai maido amsa ba.

Share.

game da Author