BABBAN SALLAH: Allah yayi wa Najeriya Albarka – Sarkin Kano

0

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II yayi kira ga gwamnatin Najeriya da yan kasuwa da su kirkiro hanyoyi domin samar wa mutanen Najeriya sauki musamman kan abubuwan da ya shafi kayan masarufi da na abinci.

Sarki Sanusi ya fadi haka ne bayan sauka da ga hawan Sallah a birnin Kano.

Ya ce lallai mutanen Najeriya na cikin matsatsi na rayuwa musamman na abincin ci da na masarufi da suke bukata.

Ya roki Allah da ya sanya Albarka a noman da aka yi bana.

Daga karshe ya yi kira ga jama’a da su kula da gyaran muhallinsu don kauce wa cututtuka musamman zazzabin cizon Sauro.

Share.

game da Author