Ba za a rusa shingen binciken motoci na hanyoyi a Abuja ba – Rundunar ‘Yan sanda

0

Rundunar ‘yan sandan Abuja ta ce za ta ci gaba da amfani da shingen binciken shige da fice a garin Abuja.

Kakakin rundunan ‘yan sandan Abuja Anjuguri Manzah ya sanar da hakan ranar Laraba wa manema labarai.

Ya ce hakan zai taimaka wa rundunar kama masu aikata miyagun aiyukka musamman barayin motoci.

” Rundunar ‘yan sandan Abuja ba za ta iya yin biyayya ga umurnin shugaban ‘yan sanda ba na rusa duk shingen binciken shige da fice a Abuja.”

Daga karshe ya yi kira ga mutane musamman masu motoci da su saka na’urorin kariya a cikin motansu domin rage sace-sacen da ake yi a Abuja.

Share.

game da Author