Ba mu yadda da afuwar da Tambuwal yayi wa mutanen da muka kama da laifin cin hanci ba – Hukumar EFCC

0

Hukumar EFCC ta daukaka kara a Sokoto domin nuna rashin amincewarta kan afuwan da gwamnan jihar Aminu Tambuwal ya wa wasu, Tukur Alkali, Bello Isah, Isah Sadiq, Habibu Halilu Modachi da Muhammadu Dingyadi.

Hukumar EFCC ta kai su kotu ne bayan an kama su da laifin aikata cin hanci da rashawa.

Hukumar EFCC ta ce bisa ga dokar Najeriya gwamnan jiha ba shi da ikon dakatar da sauraron karan mutanen da hukumarsu ta gurfana.

Hukumar ta ce gwamnan jiha zai iya yin hakan bayan kotu ta kammala sauraron karan amma ba a dakatar ba cewa Antoni Janar din kasa ne kawai ke da ikon yin haka.

Hukumar ta ce tsoma bakin da Aminu Tambuwal ya yi a aiyukkansu bai kamata ba musamman ganin cewa gwamnatin tarayya ce ta kafa su.

Share.

game da Author