Ba mu goyon bayan Biafra -Kasar Turkiyya

0

Kasar Turkiyya ta bayyana cewa sam ko da alama ba ta goyon bayan ballewar da kungiyar IPOB su ka nemi yi domin su kafa Biafra.

An buga wannan sanarwa ce a shafin ofishin jakadancin kasar Turkiyya na kasar Najeriya da shafin su na Facebook, mai suna Turkish Embassy Nigeria Abuja.

“Mu na sanarwa ga Najeriya da duniya baki daya cewa akwai wani dan kasar Turkiyya wanda ake nuno hotunan sa ya na alaka da Nnamdi Kanu da kuma IPOB.

“Mutumin mai suna Abdulkadir Erkahraman, ya na cewa shi jami’in diflomasiyyar Turkiya ne. To mu na sanarwa cewa ba jami’in mu ba ne, kuma ba da yawun kasar Turkiyya ya ke gudanar da mu’amalar sa ba.

” Turkiyya ta amince cewa Najeriya kasa daya ce dunkulalliya, sannan ba ta goyon bayan a raba kasar ko kokarin wani yanki ya balle.

“Don haka duk wanda ya yi hulda da shi, ba da yawun Turkiyya ya yi ba.”

Share.

game da Author