Asibitin Kashi na Kano na fama da karancin kayan aiki – Mohammad Nuhu

0

Shugaban asibitin garan kashi na kasa dake Dala jihar Kano Muhammad Nuhu ya ce asibitin na fama da karancin kayayyakin aiki sannan mutanen da suke bukatan kula a asibitin sun yi musu yawa.

Ya ce akalla mutane 10 dake bukatan gyaran kashin baya ke zuwa asibitin a kowani mako sannan yawan gadajen da suke da su guda takwas ne kawai.

Ya fadi hakan ne a taron wayar da kan mutane kan illolin dake tattare da raunin da ake samu a kashin baya da ake yi kowace shekara a jihar.

Muhammad Nuhu ya ce mafi yawa yawan raunin da ake samu a kashin baya musamman a kasashen da ake ci gaba kamar Najeriya sanadiyyar hadarin mota ne.

Daga karshe jami’a a wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Rebuilding Hope on Wheels Initiative’ Amina Audu ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gina asibiti na musamman domin kula da mutanen da ke fama da cutar kashin baya.

Ta ce a jihar Kano kawai mutanen da ke fama da wannan cuta sun kai 100.

Share.

game da Author