APC ta maida wa ministar harkokin mata martani

0

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Segun Oni, ya fito a karon farko ya yi bayani dangane da matsayar jam’iyyar su, kan furucin da Ministar Harkokin Mata, Aisha Alhassan ta yi, inda ta nuna goyon bayan ta ga Atiku Abubakar idan zaben 2019 ya zo.

Aisha ta ce Atiku Abubakar ne ubangidan ta a siyasa, kalaman da su ka haifar da cece-ku-ce a fadin kasar nan.

A nasa martanin, Oni ya nuna mamakin sa kwarai da kasassabar da Aisha ta yi. “Na cika da matukar mamaki kwarai, amma shi Shugaban Kasa da kan sa da kuma jam’iyya za su yi magana a lokacin da ya dace.” Inji shi.

Mataimakin dai ya yi wannan magana ne a filin jirgin saman Makurdi, jihar Binuwe, yayin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN.
Har yau dai kakain jam’iyyar bai ce komai ba, duk kuwa da tuntubar sa da PREMIUM TIMES ta yi.

Ita ma ministar ta ce zuwa yau ba ta yi ido-da-ido da Shugaban Kasa ba, tun bayan wannan furuci na ta, wanda da yawan masu sharhin siyasa na ganin cewa furucin nata tamkar wuka ce ta dauka ta yanka a wuyan ta, to kuma ta burma wa cikin ta.

Share.

game da Author