Maitaimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a harkar sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad ya ce lallai akwai wadanda suke yi wa shugaban kasa zagon kasa a wannan mulki nasa sai dai addu’oin da ake ta yi masa ba zai sa yinkurin su yayi tasiri ba.
Bashir ya fadi haka ne a shafinsa na Facebook a wata doguwar rubutu da yayi.
Ya ce addu’oin talakawan Najeriya ne ke taimakawa wajen ruguza yunkurin masu yi wa shugaban kasar haka.
DALILIN DA YA SA SUKE YI WA BABA BUHARI ZAGON-KASA
Lalle akwai masu yi wa Baba Buhari zagon-kasa, amma addu’ar talakawa masoyan sa kuma masoya Nigeria ba zata taba bari yunkurin su yayi tasiri ba alfarmar Fiyayyen Halitta.
Bayan samun lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari lalle bai kamata mu tsaya da yi masa addu’o’in alkhairi ba, akwai aiki mai dubbin yawa a gabansa, akwai kuma mutane masu yawa da ba su fatan ganin yayi nasara.
Shugaba Buhari a koda yaushe fatansa shi ne ganin talakawa sun fita daga cikin kangin wahala, sun amfana da dukiyar da Allah ya horewa kasar su Nigeria, amma irin wadanna mutane burin su shi ne a kullum su ga talakawa na kara fadawa cikin wahalhalun rayuwa, wannan dalili ya sa suka yi damarar yaki da Baba Buhari, yakin da ba zasu yi nasara ba da yarda Allah.
Martanin Baba Buhari a yau kan labarin fitar Nigeria daga kadamin kangin tattalin arziki shi ne, ya nuna farin cikin sa da nasarar da aka samu, amma sai ya ce aiki ko kadan bai kare ba har sai lokacin da talakawa suka tabbatar da hakan ta hanyar samun saukin yadda suke tafiyar da rayuwar su ta yau da kullum.
Zan yi amfani da wannan dama na roki ‘yan Nigeria musamman masoya Baba Buhari da mu ci gaba da sa shi cikin addu’o’in mu kan Allah ya ba shi nasara kan duk wasu masu yi wa gwamnatin sa zagon-kasa na fili da na boye.
– Bashir Ahmad
P.A New Media