Masu garkuwa da mutane sun sace wasu amare a hanyar su na zuwa wurin bikin auren su.
Barayin sun tare amaren ne a hanyarsu na zuwa garin Okene.
Da suka tare su sun tasa keyar Ango da Amarya da dukka kawayen Amarya da babban abokin Ango zuwa cikin kungurmin daji.
Daga baya dai mahaifin amaryan ya ya ce masu garkuwan sun saki Amaryan da kawarta amma har yanzu Ango na hannu.