Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana a ranar Lahadi cewa, masu garkuwa da mutane sun sako daraktan Ma’aikatar Ilimi na jihar wanda masu garkuwar su ka kama.
Kakakin yada labarai na rundunar, Muktar Aliyu ne ya bada wannan tabbacin da yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, a Kaduna.
Ya kara da cewa an sako daraktan tun safiyar Lahadi, kuma tuni ya na tare da iyalin sa.
Aliyu ya kara da cewa ita ma wata mata mai shayarwa, wadda aka sace tare da daraktan da ke makwabtaka da shi a unguwa daya, an sake ta. An dai sace mai jegon ne kuma aka gudu da ita ba tare da jinjirin ta makonni uku da haihuwa.
Sai dai kakakin ‘yan sandan bai yi wani bayani ko an biya diyya ba.
Aliyu ya roki jama’a da su rika bai wa jami’an tsaro bayani yadda za su rika kawo agajin gaggawa domin kauce wa afkuwar irin haka.
Kamfanin Dillancin Labarai ya taba buga labarin yadda aka yi garkuwa da John Gorah, aka sace shi tsakar dare, a ranar 3 Ga Satumba, 2017, a gidan sa da ke Mararaban Rido, Kaduna, daga baya wadanda su ka yi garkuwar da shi, su ka kira iyalan sa inda su ka bukaci sai an biya naira miliyan goma kafin su sake shi.