Rahotanni sun tabbatar da cewa an sace wani Mataimakin Kwamishinan ‘’Yan sanda, mai suna Emmanuel Adeniyi, a dajin Birnin Gwari zuwa Funtua.
Daily Trust ta ruwaito cewa an sace shi ne tare da iyalin sa a ranar Labara a lokacin da ya ke tafiya a cikin mota kirar Toyota Hilux.