Bukin Babbar Sallah ya bar baya da kura a kauyen Durumin Biri cikin Karamar Hukumar Kafur a Jihar Katsina, yayin da wani Bafulatani ya rasa ran sa a gasar neman auren budurwa.
Majiyar rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cewa mamacin mai suna Inusa, ya sha duka ne a wasan sharo, a hannun abokin hamayyar sa Ahmed Sa’idu.
“Inusa ne ya fara cauda wa Sa’idu tsabga a ciki da kuma baya. Maimakon Sa’idu ya rama dukan a inda aka doke shi, sai ya rafka masa sanda a kai.’
Majiya ta ce nan take Inusa ya fadi somamme. Ba a jima ba kuma ya mutu a cikin fage, a gaban dimbin ‘yan kallo.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kara da cewa:
” Baban Inusa ne da kan sa ya kawo kara, inda jami’an mu su ka kamo Sa’idu.”
Ya kara da cewa tuni an damka gawar Inusa ga iyayen sa, har an sallace ta.
Sharo dai al’adar Fulani ce, da yawa na gwada jarumtar auren budurwar su a wurin wasan sharo.