An kama wani tsoho dan shekara 70 da laifin yi wa wata yar shekara 7 fyade sau da yawa

0

Wani tsoho dan shekara 70 ya ce dalilin giya da yake sha ya bugu ne ya sa ya ke yi ma wata yarinya yar shekara 7 fyde duk lokacin da suka hadu.

Tsohon mai suna Papa Eke wanda aka mika shi gaban yan sanda ya ce sau biyar ne kawai ya yai wa yarinyar fyade kuma yana yin haka ne bayan ya bugu da giya.

Wannan aiki ya faru ne a jihar AkwaIbom.

Da wanda take goyon yarinyar ta ke mai da Magana ta ce ta gano cewa yarinyar bata da lafiya ne da ta lura cewa tafiyarta ya canza sannan tana yawan cewa mafitsaranta na mata ciwo.

Da ta tambaye ta shine ta gaya mata cewa wai wannan tsoho ne yake danne ta shekara kusan uku Kenan yana yi mata fyade.

Ta ce bayan haka ya yi mata balli-balli a bayanta inda ya goga mata magani wai don kar ta fadi wa iyayenta.

Uwar goyon nata tace da kyar yarinyar ta iya fada musu abin da ke faru har ya kai ga aka kama wannan mutumi.

Share.

game da Author