An kama kwamandan Boko Haram da ake nema ruwa-jallo

0

Hukumomin Tsaro na sojijin kasar nan sun bayyana cewa an damke wani kasurgumin kwamandan Boko Haram, wanda ake ta nema ruwa-jallo.

Hukumar ta ce a jihar Ondo ne rundunar ‘yan sanda ta kama kwamandan mai suna Idris Ibrahim Babawo, da ke kiran kan sa Idoko, ko Nagada, kuma shi ne lamba 156 na jerin hotunan manyan Boko Haram da jami’an tsaro na sojoji ke cigiya tun a cikin 2016.

Kakakin rundunar sojojin kasar nan, Sani Kukasheka ne ya bayayyana labarin kama Babawo, a lokacin da yak e jawabi a Maiduguri. Ya ce shekarun Babawo 42 da haihuwa.

Burgediya Janar Kukasheka ya ce tuni ‘yan sanda sun damka wanda aka kama din ga jami’an sojoji.

Ya ce an cafke shi ne da misalin karfe 2 na ranar Lahadi, 24 Ga Satumba, 2017, inda washegari su ka damka shi a hannun Bataliyar Sojoji ta 32 ta jihar Ondo.

Binciken farko ya tabbatar da cewa wanda aka cafke din dan asali kauyen Chinade ne, karamar hukumar Katagum ta jihar Bauchi.

Ya kuma kara da cewa Babawo ya gudu zuwa jihar Ondo ne sakamakon matsin da Boko Haram ke fuskanta daga sojojin Nijeriya a Arewa maso Gabas.

Share.

game da Author