An gano wani kamfanin kera makamai a Abuja

0

A yau Juma’a ne rundunar ‘Yan sanda ta sanar da gano wani kamfani da ake kera bindigogi a kauyen Ahenagu dake kusa da Zuba Abuja.

Kwamishinan ‘Yan sandan Abuja Sadiq Bello ya sanar da hakan wa manema labarai inda ya kara da cewa sun kama mutane uku.

A binciken da suka yi ya nuna cewa wani mai suna Philip John ne ke da mallakin kamfanin. Da Onyegabueze Okpara da Joseph Bulus su na kamar abokan harkallar sa ne.

Sadiq Bello yace sun kama bindigogi da harsashai da yawa a samamen.

Yayin da ‘yan sandan ke gudanar da bincike John ya ce ya yi shekaru 17 yana wannan sana’ar. Ya ce ya kan siyar da bindigan da ake kira ‘Single-barrel’ akan Naira 20,000 da wanda ake kira ‘Dane’ akan Naira 10,000.

Shi kuwa Okpara wanda ke canza kamanni da sana’ar siyar da kayayyakin keke yana siyar da bindigogin ne a kasuwan Kaita wa masu aikata munanan aiyukka sannan Bulus kuma an kama shi a Zuba tare da makaman da yake siyarwa.

Daga karshe Sadiq Bello ya ce za su kai su kotu bayan sun kammala bincike akan su.

Share.

game da Author