AMBALIYA: Shugaban hukumar NEMA ya tafi jihar Benue

0

Babban Daraktan Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA ya isa jihar Binuwai domin tantance irin barnar da ambaliya ta yi wa jihar.

Mustapha Maihaja ya shaida wa Gwamnan Jihar cewa ya isa Makurdi ne a bisa umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin ya tantance irin ta’adin da ruwa ya yi, ta yada gwamnatin tarayya za ta san irin daukin gaggawar da za ta yi.

Maihaja ya ce an turo motoci dankare da kayan tallafin abinci ga wadanda wancan mummunar ambaliya ya kassara. Ya kuma kara yin albishir cewa akwai wasu motocin dauke da wasu kayan agajin da ga Abuja, wadanda ya ce nan da kwana uku za su isa Binuwai.

Da ya ke maraba da Babban Daraktan, Gwamna Samuel Ortem ya jinjina wa Shugaba Buhari ganin yadda ya gaggauta kai agaji da tallafi ga Jihar Binuwai.

Share.

game da Author